DAGA: ZAINAB INDOMIE!!!
TARIHINA A TAKAICE:
Assalamu alaikum da farko dai
sunana Zainab
Abdullahi, wacce aka fi sani da
Zainab
Indomie. Ni cikakkiyar Bahaushiya
ce, an
haife ni a Abuja kuma ina zaune a
Abuja. Na
yi makarantar Firamare da
sakandare a Abuja,
sannan na yi difloma a kan Ilmin
Kimiyyar
Kwamfuta a Kaduna.
YADDA NA FARA HARKAR FILM:
Ka san babu yadda Allah ba Ya yi da
mutum.
Tun ina karama nake sha’awar
kallon fina-
finan Hausa. Ina jin dadi idan ina
kallon fina-
finan Hausa. Wannan ne ya ja
hankalina, ya
sa na yi burin a rika damawa da ni
a harkar. A
haka na tsinci kaina a harkar wanda
har
zuwa yanzu na zama wata aba a
duniyar
fina-finai.
Kafin na shiga harkar fim na yi fadi-
tashi
sosai. Ina cikin fadi-tashin ne Allah
Ya hada ni
da Ali Nuhu, bayan na fada wa
iyayena sun
amince sai suka damka ni a
hannunsa a
matsayin amana. Daga nan ne ya
yarda ya
kuma rika sanya ni a cikin fina-
finansa. Ba ni
da wani ubangida a harkar fim da
ya wuce
Ali Nuhu har yau kuma har gobe.
Ya ma wuce
ubangida ya zama uba kuma dan
uwana. Fim
din da na fara ko kuma na ce
wanda ya
haskaka ni shi ne ‘Garinmu Da Zafi’.
Wannan
fim din shi ne fim din da na fi so
duk a cikin
fina-finan da na yi.
YADDA NA SAMU LAQABIN
INDOMIE:
Na san mutane da yawa za su so
jin yadda na
samu lakabin ‘Indomie’ da kuma
wurin da na
same shi. Wannan sunan ya samo
asali ne tun
ina firamare. Tun a lokacin babu
abincin da
na fi so kamar taliya, hakan ne ya
sa na
daukaka taliyar Indomie a kan
kowane irin
nau’in abinci. Wannan dalilin ne ya
sa aka
fara kirana da lakabin ‘Indomie’.
DALILIN DA YASA KUKA GA NA
RAME:
A baya idan mutane za su iya
tunawa na yi
jiki sosai, a gaskiya idan har kana
da jiki to za
ka sha wahala wurin gudanar da
sauran
ayyuka musamman ma mu ‘yan
fim. Idan
akwai wani rol wanda ya shafi rawa
ko gudu
ko tsalle-tsalle, to dole idan har
kana so ka
sake, ka ji dadin jikinka sai idan ba
ka da kiba,
domin idan kana da kiba bayan an
gama za
ka ji ka wahala sosai, sannan ba za
ka yi rol
din yadda ake so ba. Don haka ba
wai jinya
ko tashin hankali ko tunani ko
yunwa ba ne
suka sanya na rame ba, a’a, na
rage kiba ne,
wanda ake kira ‘slimming’ da
Turanci kenan.
HOTUNAN TSIRAICIN DA KUKE
GANI NAWA:
A gaskiya ban san da su ba, mutane
ne kawai
suke yi don su bata mini suna. Ana
yin hakan
ne don a durkusar da jarumi don a
daina yi
da shi. A ce taurarinsa sun
dusashe, amma
duk wannan abin da ake yi mini
Allah bai sa
taurarina sun dusashe ba. Ana
sona kuma
masu kaunata ba su daina ba. Babu
abin da
zan ce ga masu yi mini wannan
abin sai dai
Allah Ya saka mini. Ka lura duk
wanda ya ci
gaba ko ya samu daukaka sai ya
fuskanci irin
wadannan abubuwa.
RASHIN FITOWA A FINA-FINAN
KWANAN NAN:
Na san mutane za su ce a yanzu an
daina yi
da ni, to su sani ba haka ba ne.
Idan ba za ka
manta ba a baya na ce maka na yi
difloma a
Kaduna, kuma kowa ya sani taura
biyu ba za
ta taunu ba. Hakan ya sanya na
ajiye harkar
fim har sai da na kammala
karatuna, amma
nan ba dadewa ba masoyana za su
fara
ganin sababbin fina-finaina.
To kun dai ji abinda tace,
Via: Rariya...
No comments:
Post a Comment