KE: Da farko dai wanene kai?
Sunana Yusuf Ahmad Nahuche
(Marafa) an haifeni a 1985 a garin
nahuche ta karamar hukumar mulkin BUNGUDU dake jahar zamfara. Nayi primary na a
Nahuche 01 model primary school, daga nan na wuce government technical college
kaura namoda, inda nayi secondry school dina, a shekarar 2008 naje abdu gusau polytechnic talata
marafa (zamfara state) anan nayi diploma fannin architecture, bayan dana kammala
saina wuce waziri umaru federal polytechnic a shekarar 2011 inda na karanta HND
quantity surveying........wanda yake yanzu ina jiran tafiya bautar kasa ne,
wannan shine takaitaccen abinda ya shafi tarihin tashina a rare da kuma
karatuna
KE: Toh mallam yusuf meya janyo ka harkar film?
SHA'AWA! Tun ina primary skul na
kasance mai sha'awar karance karancen littafan hausa, bazan manta ba akwai wani
malamina mai suna Muhammad Maiyaki (Malam J.B) yakan zaboni ya bani littafin
hausa yace na karantawa dalibai, a duk ranar daya gayyaceni wannan aiki na kan
zama sarki a ajinmu, domin kujera ake kawoman na zauna ina karantawa dalibai na
saurarena, idan na gama yakan bani kwandala biyu, uku watarana har naira biyar,
a haka naci gaba da karance karancena, harnaje secondry, lokacinda nakai aji
biyu na secondry saina fara karban rented na littafan hausa ina karantawa
kasancewar karatunsu ya shiga jini na, a haka naci gaba harna kare, sai dai tun
a wancan lokacin nake sha'awar yan film, wasu lokuta idan ina karatu saina rika
danganta abinda nake karantawa da yan film, wasu lokuta saina zauna ina tunanin
inama ace watarana na hadu da ali nuhu? Inama ace watarana nima na zama dan
film? haka na rayu tsawon lokaci da wannan kudurin araina, wanda daga baya har
allah ya cikaman burina na fara harkan kamar yanda nake tsarawa a zuciyata
KE: To ko za ka iya gayamana wasu daga cikin fona finan da
ka rubuta?
Na rubuta adadinsu ne takarda,
amma bazan iya ganewa ba face na duba takardar, amma ga wadanda nake iya
tunawa: Ramlat, Soyayya da Shakuwa, Kurciya, Zurfin Ciki 2 and 3, Ranar Aurena,
Martani, Izaya, Kaidin Mace, Aurena Dake, Makauniyar Hanya, Balaraba, Matar
Bahaushe, Dan Adam, Saki Kowa, Babbar Rana, Zarge, Raddi, Wani Mutum, Zanen
Dutse, Babbar Rugga, Mun Shaku da Juna, Shine Riba, Yar Uwata, Gurguwa Mai
Naira, Ummu Sulaim, Wani Lokaci, Naira da Kwabo, Wutar Kara, Mulkin Mallaka,
Gida Daya, Ina Zaki Damu, Gangar Jiki, Bani Ba Aure, Kungiya, Kasuwar Mata,
Makahon So. Da sauransu, wadannan suna
daga cikin fina finan dana rubuta, wasu sun fita kasuwa, wasu ana daukarsu
yanzu haka, wasu kuma ana shirye shiryen fara daukarsu
KE: To mallam yusuf kana rubuta manyan fina-finai. Ko za ka
gaya mana me ya kawo nasaran haka
Bana nufin alfahari, sai dai ina
nufin yin godiya ga ubangijina, ni kaina nasan ina samun nasara, amma na
danganta hakan da Addu'ar da nake samu daga iyaye da sauran mutane masu
kaunata, haka iya mu'amala da mutane yayi tasiri wajen samuwar nasarata
KE: Mallam yusuf akwai masu san rubuta labarai amma basu
san wata hanya za su bi ba, ko akwai wani shawara da za ka iya basu?
Naji dadi daya kasance akwai masu
sha'awar rubutu, hakan yayi nuni da cewar rubutu na samun karbuwa a wurin
al'ummarmu, shawarata ga masu wannan kuduri itace su rike aniyarsu kada su
gaza, su cigaba da fadada aniyar tareda fatan samun nasara ko yaushe, su kuma
kusanci wadanda suke cikin harkan domin samun taikonsu, haka kuma su kasance
masu bincike da kirkira domin samun ingantaccen aiki
KE: Mun samu labari cewa film din kannywood
"MAJA" ya samu shiga rukunai hudu a gasar samun kyauta na KEA2014
wanda ya kasance shi kadai ne ya sami shiga har rukunai huda, kuma masu bin sa
fina finan Noolywood ne guda biyu. Shin kanaga hakan ya nuna cewa fina finan
hausa na bunkasa ne? Ko dai dan an sa dan Nollywood a cikin fim din ne?
Fina finan hausa suna bunkasa a
zahiri, idan ka waiwaya baya na daga shekarun da suka gabata, zakaga cewar duka
duka shekarun kafuwar masana'antar fina finan hausa bata jima ba, amma gashi
zuwa yanzu ayukanmu suna inganta kuma suna samun karbuwa, a yanda nake ganin
yanayin cigabanda aka samu a fina finan hausa, bana shakkar shigarda ko wane
film a fagen gasa, ba MAJA kadai ba, akwai fina finai da dama da za'a iya
sakawa a fagen gasa kuma su ciri tuta, saboda haka hausa film industry tana
samun cigaba ta kowane fanni
KE: To mallam yusuf a fina finan da ka rubuta wanne kafi so
kuma meyasa?
SOYAYYA DA SHAKUWA! Saboda shine
film dinda na rubutashi ina maijin dadin rubutun, labarin yayiman dadi, kuma an
dauki shirin yanda ya dace, bazan manta ba a ranar da aka kammala aikin film
din saida na kira Adam A. Zango ya fadaman nasararori da kuma cikas din da suka
samu ga aikin, hikima tayin hakan shine domin in sani shin labarin ya tafi bisa
tubalin dana rubutashi akai? Alhamdullahi anyi nasara wurin aikin, shiyasa naji
film din ya shiga raina sosai
KE: To ko za ka iya gaya mana kalubalen da ka fuskanta a
wannar harkar.
Na fuskanci kalubale mai yawa
kafin na samu karbuwa, kalubalen farko dana fara fuskanta shine: ranar dana
fara zuwa kano da zummar fara wannan a ranar mukayi hatsari da dan achaba,
gashi bansan kowaba a kano, Maje El-hajij shiya fara taimakona harna samu na
wartsake, daga nan saina fara fuskantar wulakanci daga wurin masu dama a
hannunsu, wanda yake daga baya kuma sun dawo sun nuna nine nasu
KE: Me za ka cewa yan uwa da abokai wanda suka goya ma baya
a harkan nan
Ina godiya garesu duka, sun
taimakeni a rayuwata, kuma har yanzu ina tafiyane bisa tubalin da suka dorani
akai, wasu sun taimakeni a zahiri, wasu a badini, wasu shawara suka bani, wasu
addu'a sukayi man, duka dai ina godiya da gudumawarku a tsarin rayuwa
KE: To kafin mu rabu wani babban shiri ka ke kan rubutawa
ko ka gama ruburawa a kwanakin nan
Rubutu na karshe dana gama shine
AURENA DAKE! Yanzu kuma zan fara SO daga ALLAH
KE: To madallah mun gade da lokacin da ka bamu kuma Allah
ya kara basira da sa'a
Amin nima nagode da kulawarku
No comments:
Post a Comment