Showing posts with label Writer. Show all posts
Showing posts with label Writer. Show all posts

Sunday, February 1, 2015

Full List of Winners - MTN Kannywood Awards 2014







This is the full list of winners from the MTN Kannywood Awards wich was concluded early Sunday 1st February 2015.
The awards saw most of the big names going home with prizes, and other very big names left out. The late Rabilu Musa Dan ibro won Two awards, Best Comedian Popular Choice and Best comedian Juror’s award
Other popular acts like Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Hadiza gabon and Fati Washa also went away with awards. Other big names that left out are Adam A Zango & Rahma Sadau. But below is the full list of winners
POPULAR CHOICE CATEGORY
·  Best Actor - ALI NUHU
·  Best Actress - NAFISAT ABDULLAH
·  Best Director - YASIN AUWAL
·  Best Comedian - Late RABILU MUSA (IBRO)
JUROR’S AWARDS
·  Best Actor: SADIK SANI SADIK for Dinyar Makaho
·  Best Actress: HADIZA GABON for Daga Ni Sai Ke

Friday, June 6, 2014

Hira da Marubuci Yusuf Ahmd Nahuce (Marafa)




KE: Da farko dai wanene kai?

Sunana Yusuf Ahmad Nahuche (Marafa) an haifeni a 1985 a  garin nahuche ta karamar hukumar mulkin BUNGUDU dake jahar zamfara. Nayi primary na a Nahuche 01 model primary school, daga nan na wuce government technical college kaura namoda, inda nayi secondry school dina, a shekarar  2008 naje abdu gusau polytechnic talata marafa (zamfara state) anan nayi diploma fannin architecture, bayan dana kammala saina wuce waziri umaru federal polytechnic a shekarar 2011 inda na karanta HND quantity surveying........wanda yake yanzu ina jiran tafiya bautar kasa ne, wannan shine takaitaccen abinda ya shafi tarihin tashina a rare da kuma karatuna

KE: Toh mallam yusuf meya janyo ka harkar film?

SHA'AWA! Tun ina primary skul na kasance mai sha'awar karance karancen littafan hausa, bazan manta ba akwai wani malamina mai suna Muhammad Maiyaki (Malam J.B) yakan zaboni ya bani littafin hausa yace na karantawa dalibai, a duk ranar daya gayyaceni wannan aiki na kan zama sarki a ajinmu, domin kujera ake kawoman na zauna ina karantawa dalibai na saurarena, idan na gama yakan bani kwandala biyu, uku watarana har naira biyar, a haka naci gaba da karance karancena, harnaje secondry, lokacinda nakai aji biyu na secondry saina fara karban rented na littafan hausa ina karantawa kasancewar karatunsu ya shiga jini na, a haka naci gaba harna kare, sai dai tun a wancan lokacin nake sha'awar yan film, wasu lokuta idan ina karatu saina rika danganta abinda nake karantawa da yan film, wasu lokuta saina zauna ina tunanin inama ace watarana na hadu da ali nuhu? Inama ace watarana nima na zama dan film? haka na rayu tsawon lokaci da wannan kudurin araina, wanda daga baya har allah ya cikaman burina na fara harkan kamar yanda nake tsarawa a zuciyata

KE: To ko za ka iya gayamana wasu daga cikin fona finan da ka rubuta?

Na rubuta adadinsu ne takarda, amma bazan iya ganewa ba face na duba takardar, amma ga wadanda nake iya tunawa: Ramlat, Soyayya da Shakuwa, Kurciya, Zurfin Ciki 2 and 3, Ranar Aurena, Martani, Izaya, Kaidin Mace, Aurena Dake, Makauniyar Hanya, Balaraba, Matar Bahaushe, Dan Adam, Saki Kowa, Babbar Rana, Zarge, Raddi, Wani Mutum, Zanen Dutse, Babbar Rugga, Mun Shaku da Juna, Shine Riba, Yar Uwata, Gurguwa Mai Naira, Ummu Sulaim, Wani Lokaci, Naira da Kwabo, Wutar Kara, Mulkin Mallaka, Gida Daya, Ina Zaki Damu, Gangar Jiki, Bani Ba Aure, Kungiya, Kasuwar Mata, Makahon So. Da sauransu,  wadannan suna daga cikin fina finan dana rubuta, wasu sun fita kasuwa, wasu ana daukarsu yanzu haka, wasu kuma ana shirye shiryen fara daukarsu