An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar
1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan
da
ke cikin karamar hukumar Warawa.
Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon
malamai ta Wudil (Teachers College).
Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison
Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas
Ya
na aikin Gandiroba inda ya kai matakin insfekto,
daga nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan
kwaikwayo.
Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim a tun ya na
aji uku na makarantar sakandare.
Ya na da Mata uku da yara
Matan sune:
Jamila, Kubra, Auta.
Daga cikin yaransa akwai: Akwai Faisal, Jawahid,
Lawiza, Abdul-Mummuni, Sannan akwai Asma’u,
Annabe, Sa’adiyya, Akwai wani yaro kuma da ya
Haifa ya sa sunan mai gidansa wato Baba Yaro.

dan wasan hausa abokin sana’ar sa da ya fi
burgeshi.
Da aka tambayi Rabilu Musa ibro dan wasan
santimental da ya fi burgeshi sai yace “ Adamu
Usher, ka ga wannan, yana bani sha’awa. Saboda
ba shi da girman kai, ba zan manta ba lokacin
rasuwar kulu da Yautai, tun daga farkon rasuwar
mu na tare da su.” In ji Ibro
Daga cikin dubunnan fina finansa ibro ya
bayyana
cewa ya fi son wadannan fina finai “Akwai
Kauran
Mata, Kowa Ya Debo Da Zafi, da kuma Mai Dawa.
Ibro ya bayyana ya fi son tuwon dawa a
bangaren
abincinsa, fannin sutura kuma sai yace “Na fi
son
yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba
in
sa Shadda ba kwana biyu in ga tana kodewa.
Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na
raye
me ya fi bakanta masa rai a kan harkar
sana’arsa
sai yace“ Ni abinda yake bata mani rai kawai a
wannan sana’a bai wuce rashin hadin kan ‘yan
wasa ba.
Rabilu Musa Ibro Ya amsa kiran mahallicinsa ya
na
da shekaru 43, a duniya. Allah ya kyautata
makwanci.
Allah ya gafartamasa, kuma in muma lokacin mu yayi, Allah ka sa mu cika da Imani #Ameen
No comments:
Post a Comment