A
cikin kalamai wanda aka saka ma gidan jarida na Pulse kawai, Rahama ta
yi bayanai akan wannan magana, kuma ta nuna jin ciwon zuciya ga wanda ya
ƙaga wannan rikodi akan WhatsApp. Ta yi umarni cewa kada mutane su
yarda da wannan hira. Ga kalamai
"Bayan
an baza wani wasiƙa (a watan Oktoba 2016) cewa an fitar da ni daga
wasan kwaikwayo a Kannywood, ba zato ba tsamani, wasu mutane sun ƙera
wani rikodi na murya akan shafin WhatsApp. Sun yayata cêwa an jarabce ni
in canza addini. Bugu da ƙari, sun cê an bani milyoyin dala da kuma
mukaddashin rawa a Hollywood. Wannan ƙaryan da aka yi mana ya janyo
hankalin ƙuriʼa na hukunci daga mutane.
Abin
baƙin ciki shi ne cêwa dattawa wanda muke girmamawa, da kuma Mallamai,
sun ci gaba da rubuce-rubuce akan wannan jita-jita a shaffufukan
yanan-gizo, ba tare sun bincika gaskiyan wannan labari. Wasu sun
shawartar ni, wai kada in tafi da wannan jarabobi. Ina baƙin ciki sosai
game da wannan zargin da akayi mana, da kuma irin sharhi wanda na
saurara daga bakin dattawan alʼumma, da kuma Mallamai. Ba su kira ni
domin su tabbatar da gaskiyan wannan jita-jita.
Iyalina
da abokan harka sun ji tuntuɓen sabili da wannan lamari. Shi ʼya sa na
ɗauki matakin bayyana wannan batu a fili. Ina son in yada haske tantama
ko kadan cêwa wannan bayanin da ake yadawa bai da inganci, kuma babu
gaskiya cikin wannan hira. Wannan labari, matalaucin koƙari ne na ɓata
mini suna da kuma sukar mana hali.
Duk
ayyukan da nake yi a kowane wuri cikin duniya, yana akan dokar sanaʼa
da kuma fasaha. Ba zan taɓa yin ciniki da Imani ko addini. Kuma addini
na ba ya taɓuwa ga duk magana, sharuddan da yanayi, ko kuma shaʼanin
aiki. Abin ɓacin rai shi ne cêwa an jawo Akon, wanda yake ɗan ƙasar
Senegal, cikin wannan lamari. Akon Muslumi ne, kuma shuni ne a kasar
Senegal. Wasu ʼƴan jarida da kuma Mallamai suna kiransa Kaffir.
Ko
da yake, wanda ya ƙero wannan rikodi akan WhatsApp bai faɗi sunansa ba,
ana cikin bincike-bincike domin gane mahallicin wannan rikodin. Ina
roƙon wadanda suke rarraba wannan rikodi na karya, su dena. Ina roƙon
maʼaboci da iyali da kuma masu yi mana fatar alheri, su ci gaba da
goyon-bayansu. Duk inda sanaʼa zai kai ni, zan tabbatar da shaidawa cewa
ni ʼyar Afrika ce, ni ʼyar Najeriya ce, kuma zan ci gaba da ayyuka
wanda zai ɗaukaka alʼadunmu.
Za
ku tuna cêwa an kore Rahama daga Kannywood bayan Ƙungiyar masu hotó da
wasaʼn Ƙwaikwaiƴo sun dakatar da ita domin wasan da ta yi tare da
ClassiQ, wani mawaƙi wanda yake garin Jos.
Bayan
an dakatar da Rahama, Jeta Amata da Akon sun gayyace ta zuwa Hollywood,
domin yin sabon fim mai suna "The American King".(Waton "Sarikin
Amirka").
Source: pulse.ng
Allah shi taimaka ...gat your back on this one
ReplyDelete