A
cikin kalamai wanda aka saka ma gidan jarida na Pulse kawai, Rahama ta
yi bayanai akan wannan magana, kuma ta nuna jin ciwon zuciya ga wanda ya
ƙaga wannan rikodi akan WhatsApp. Ta yi umarni cewa kada mutane su
yarda da wannan hira. Ga kalamai
"Bayan
an baza wani wasiƙa (a watan Oktoba 2016) cewa an fitar da ni daga
wasan kwaikwayo a Kannywood, ba zato ba tsamani, wasu mutane sun ƙera
wani rikodi na murya akan shafin WhatsApp. Sun yayata cêwa an jarabce ni
in canza addini. Bugu da ƙari, sun cê an bani milyoyin dala da kuma
mukaddashin rawa a Hollywood. Wannan ƙaryan da aka yi mana ya janyo
hankalin ƙuriʼa na hukunci daga mutane.










