Wakilin mu ya sami Magana da Ali Artwok, wanda a kwanakin
baya ya kara karfin wutan sa’insar da ke tsakanin Rahma Sadau da Adam A Zango,
bayan zagin ali nuhu da yayi. Ga hirar tamu
MUN SAMU LABARIN CEWA ALI NUHU YASANYA AN KAMAKA AN KULLEKA A POLICE
STATION, MINENE GASKIYAR LABARIN KUMA MI KAYI MASA?
Ali Art: Da farko abinda ya faru Rahama sadau ce ta zagi Adam a zango
mai gidana a shafin instgram, wanda hakan ya tun zurani nikuma naji
zafin abun, saaboda naga babu wani babba ko wata kungiyar Film wanda
sukayi magana a Lokacin da Abin ya faru sai nima nakoma naje a shafin
instgram din na zagi Ali nuhu da ita Rahama, kuma na gaggayata mata
maganganu.
TO KAI MINENE KA RUBUTA A SHAFIN NA INSGTRAM?
Ali Art: Eh nayi Rubutu kamar Haka: "ALI NUHU YANA DAUREWA KANANAN
YARA GINDI SUNA ZAGIN MANYAN MUTANE, SABODA HAKA MU BAZAMU IYA ZUBA
IDO BA, A MATSAYINSA NA BABBA WANDA ZAI HANA AMMA SHI YAKE BADA UMARNI
SABODA HAKA BAZAMUYI DASU BA SAI DAI MUYI DASHI. @Aliartwork to
Real_Alinuhu Kai Babban Banza ne! Da kace Rahama Sadau ta zagi Adamu
minene Ribarka? Wato kagane kayi mata film takiyin suna shine kace ta
biyo ta haka.. Kai wai miyasa Baka kaunar a zauna Lafiya? Wannan
abinda kakeyi da sunan kai mai Ilimine, To inaso kasan jahilcine! Kuma
wawancine, domin dama na dade da sanin cewa kai munafiki ne, mai fuska
biyu, ga ka da suffara mutane amma dabi'unka na Dabbobine, wadanda
kake sakawa suna zagin @de_prince_zango basu fi karfin mu suburbudasu
ba, shiyasa muka fara dakai, saboda mu nuna masu cewa kai ba komai
Bane, idan har bazaka chanza halinka ba, to muma munanan kamar yarda
kasani babu girmamawa a tsakaninmu kuma kada kasake tunanin idan mun
hadu dakai zamu sake baka wani girma ko matsayi Banza jaki dakai nake
Ali Nuhu kamar yadda Rahama sadau tace Fuck @de_prince zango to kaima
Fuck ur Mother...
Wannan shine abinda na Rubuta wanda hakan yajawo ni nawa yai zafi amma
ita Rahama sadau kasanshi Adamu daman mutum ne mai hakuri kana iya
yimasa abu bai iya cewa komai sai yace yabar mutum ga Allah, to a
lokacin yaran Ali suka fara kirana a waya suna min barazana cewa idan
nashigo kano naga abinda zai sameni, to cikin dare sai aka kirani a
waya daga gida akace Ali nuhu ya kawo karata kan na cimasa mutunci
wannan yasa mahaifina ya kirani yayimin nashida da na zauna da abokan
aikina lafiya ba Rigima ba tashin hankali, To a daren kuma aka dawo
akaita kirana a waya to nasanya wayata silent, 'yan sanda sukazo
Gidanmu suka tararda Yayana, sukace Ali suke nema akace masu Ali yana
kaduna, suka Fiddo yayana sukaita dukansa suka daukeshi suka tafi
dashi suka kulleshi har yakawana, sai da safe naga an kirani a cikin
dare daga gida, sai na kira waya Gida ake fadamin ai jiya 'yan sanda
sunzo sun tafi da yayana akan "Case" din nan, sai nayi maza-maza na
shirya nazo kano wajen 'yan sanda nace masu nine mai laifin nan na
jiya, aka fito da yayana akasanyani cikin sel aka kulle, to wasu
mutane sukazo shiga maganar akan zanba Ali nuhu hakuri a sakeni, ni
kuma nace indai sai nabashi hakuri, gwara yasaa a yankemin duk
hukuncin da yaga ya dace, tunda daman yaso yaci mutunci iyayena da
dangina ne kawai, a ranar da akayi abun muje aikin wani Film na
(Abdul Amart) dashi a kaduna mizai hana ya turo a kamani a kadunar
tunda yasan inda nake, amma sai yasa aka kama 'yan uwana akaci masu
mutunci.
TO YANZU WANENE YAYI BELINKA DAGA HANNUN 'YAN SANDA??
Ali Art: 'yan uwana ne, sukayo Belin dina, Adam a zango yazo a Lokacin
zai shiga maganar nace masa Babu ruwanshi.
TO NAWA AKAYI BELINKA??
Ali art: ni bansan ko nawa aka biya kudin belin nawa ba, saboda Lokacin ina sel.
TO YANZU KABA ALI NUHU HAKURI KENAN??
Ali Art: Ana cikin hakan ne akace inbashi hakuri nace nima sai yaba
iyayena hakuri saboda anci mutuncinsu, to sai mahaifiyata ta sameni
tace in bashi hakuri idanma ya cuceni shida Allah, tacemin batasan
ganina a wajen, kuma hakan akayi nabashi hakuri, to daga nan ya kara
daga "case" din zuwa netro a wata police station din a zariya
Road, yana ganin yanada kudi yasan jama'a bari yasa a wulakantani
saboda banida wani gata.
ANA CEWA ADAM A ZANGO YASANYAKA KA ZAGI ALI NUHU HAKANE?
Ali art: ni adamu bai sani na zageshiba saboda a Lokacin ma baya gari
yana zaria wajen aiki, baimasan anyi ba.
TO DA ANCE AKWAI WATA ALAKA DAKE TSAKANINKU DA ALI NUHU WACE IRIN ALAKA CE?
Ali Art: ni daman ba wata Alaka tsakanina dashi, alakarmu dashi mai
Gidana Aminu Bacci shine wanda ya koyamin Editing to abokinsa ne, to
da duk fim da Ali nuhu yakeyi nine nakeyi Editing saboda ya yarda
dashi, shikuma mai Gidana ya yarda da aikina daganan muka saba da Ali
nuhu.
Kuma kodan haka bata faru ba, yakamata inyi ma Ali nuhu magana domin
yata bayimin wasu abubuwa manya guda wanda bazan taba mantawa dashiba
har yanzu abinda nayimin ciwo.
Na farko umar m sharif yataba kirana zamuyi aikin fim din jinin jikina
daga baya Ali yacewa umar kada abani aikin wani za'aba.
Na biyu kuma Lokacin da nadawo kaduna wajen adamu yake cemasa yasha
rabani rigima da mutane wai ina amsar kudin jama'a inkiyamasu aiki
wanda ba hakan bane ko wa yasani.
Daga Isah Bawa Doro (katsina) 08067880459
Gaskia wannan Rahma din ba qaramar annamimiya bace
ReplyDeleteDuk ta silarta ce ake wannan cecekuce
Mtsss
ai dama ta tabayiwa kannywood laifi wanda yafi wannan
ReplyDelete