KE: Da farko dai wanene kai?
Sunana Yusuf Ahmad Nahuche
(Marafa) an haifeni a 1985 a garin
nahuche ta karamar hukumar mulkin BUNGUDU dake jahar zamfara. Nayi primary na a
Nahuche 01 model primary school, daga nan na wuce government technical college
kaura namoda, inda nayi secondry school dina, a shekarar 2008 naje abdu gusau polytechnic talata
marafa (zamfara state) anan nayi diploma fannin architecture, bayan dana kammala
saina wuce waziri umaru federal polytechnic a shekarar 2011 inda na karanta HND
quantity surveying........wanda yake yanzu ina jiran tafiya bautar kasa ne,
wannan shine takaitaccen abinda ya shafi tarihin tashina a rare da kuma
karatuna
KE: Toh mallam yusuf meya janyo ka harkar film?
SHA'AWA! Tun ina primary skul na
kasance mai sha'awar karance karancen littafan hausa, bazan manta ba akwai wani
malamina mai suna Muhammad Maiyaki (Malam J.B) yakan zaboni ya bani littafin
hausa yace na karantawa dalibai, a duk ranar daya gayyaceni wannan aiki na kan
zama sarki a ajinmu, domin kujera ake kawoman na zauna ina karantawa dalibai na
saurarena, idan na gama yakan bani kwandala biyu, uku watarana har naira biyar,
a haka naci gaba da karance karancena, harnaje secondry, lokacinda nakai aji
biyu na secondry saina fara karban rented na littafan hausa ina karantawa
kasancewar karatunsu ya shiga jini na, a haka naci gaba harna kare, sai dai tun
a wancan lokacin nake sha'awar yan film, wasu lokuta idan ina karatu saina rika
danganta abinda nake karantawa da yan film, wasu lokuta saina zauna ina tunanin
inama ace watarana na hadu da ali nuhu? Inama ace watarana nima na zama dan
film? haka na rayu tsawon lokaci da wannan kudurin araina, wanda daga baya har
allah ya cikaman burina na fara harkan kamar yanda nake tsarawa a zuciyata
KE: To ko za ka iya gayamana wasu daga cikin fona finan da
ka rubuta?
Na rubuta adadinsu ne takarda,
amma bazan iya ganewa ba face na duba takardar, amma ga wadanda nake iya
tunawa: Ramlat, Soyayya da Shakuwa, Kurciya, Zurfin Ciki 2 and 3, Ranar Aurena,
Martani, Izaya, Kaidin Mace, Aurena Dake, Makauniyar Hanya, Balaraba, Matar
Bahaushe, Dan Adam, Saki Kowa, Babbar Rana, Zarge, Raddi, Wani Mutum, Zanen
Dutse, Babbar Rugga, Mun Shaku da Juna, Shine Riba, Yar Uwata, Gurguwa Mai
Naira, Ummu Sulaim, Wani Lokaci, Naira da Kwabo, Wutar Kara, Mulkin Mallaka,
Gida Daya, Ina Zaki Damu, Gangar Jiki, Bani Ba Aure, Kungiya, Kasuwar Mata,
Makahon So. Da sauransu, wadannan suna
daga cikin fina finan dana rubuta, wasu sun fita kasuwa, wasu ana daukarsu
yanzu haka, wasu kuma ana shirye shiryen fara daukarsu