Wakilin mu ya sami Magana da Ali Artwok, wanda a kwanakin
baya ya kara karfin wutan sa’insar da ke tsakanin Rahma Sadau da Adam A Zango,
bayan zagin ali nuhu da yayi. Ga hirar tamu
MUN SAMU LABARIN CEWA ALI NUHU YASANYA AN KAMAKA AN KULLEKA A POLICE
STATION, MINENE GASKIYAR LABARIN KUMA MI KAYI MASA?
Ali Art: Da farko abinda ya faru Rahama sadau ce ta zagi Adam a zango
mai gidana a shafin instgram, wanda hakan ya tun zurani nikuma naji
zafin abun, saaboda naga babu wani babba ko wata kungiyar Film wanda
sukayi magana a Lokacin da Abin ya faru sai nima nakoma naje a shafin
instgram din na zagi Ali nuhu da ita Rahama, kuma na gaggayata mata
maganganu.