ADAMU ZAI CIGABA DA FILM
Aslamu alaikum
Bayan doguwar tattaunawa akan matsala mafi tada hankali da ta faru jiya. Alhmdulillah, muna sanar da masoya, producers, directors cewa komai ya koma dai dai...mu sani sabanin zuciya babu abin da baya haifarwa.. duk yadda bawa yakai da hkuri tilas akwai ranar da zaa kure shi. musamman in abu yazo da zagi cin zarafi da cin mutuncin iyaye. Ina bawa masoya wannan sana'a ta film da masoyan adamu hkuri. Rasa adamu
adam a zango a industry gibi ne mai girman gaske, in dai kana san abu to ka taimake shi da addua yayin daka hangoshi cikin damuwa. Sannan jaridu masu aiki da kannywood hakkin ku ne ku kare mutunci film industry da JARUMAN cikin ta MAZA da MATA, musamman lokacin da wasu Jaridun ke yinkurin kassara Masana'antar ta hanyar canja sako mai kyau zuwa mummunan sako mara tushe su tura ga alumma. Duk abin da zaka rubuta dai dai yake da abin daka furta, in kai nufin alkairi Allah ya sani.. Allah ka tsare mu daga sharrin makiyya da Mahassada. Ameen
Sako daga Falalu A Dorayi
In baku manta ba a jiya ne jarumin ya sanar cewa ya daina fiilm sabida ya sami kwanciyar hankali. Ku karanta post dinmu na baya dan ganin cikkaken abin da ya faru